You are on page 1of 1

GIDAN SAURO .......by Poetic Tee "Here, take a sip" Haba mutum! Zaluncin na ka bai bar kowa ba?

Daga yaro ko yarinya har zuwa uwa da uba Yanzu abin na ka ya ma kai intaha Don wata katobaras sai dai ace "A'aha!" Ka kuma shiga yin dangwaliliya har ma da kwace Sam ba ka ko gudun ka-ce na-ce Sai ka karbo amanar abu don miqawa mai shi Amma a zuciyarka ba ka da niyyar yi masa adalci A bainar jama'a ka karba ko ka saya an shaida Da ka kai gida sai ka sa a shanya tun kafin shida In dare ya yi tun kafin ya tsala Mai abu ya zo ka hana shi har da shela Sai ka sa a fidda, ka kafa bacin kuma ga naka In ya yi qorafi, sai ka harare shi ka ce "Haka!" Ka shiga cikin gidansa kai da matarka Don mugunta harma da yaranka Shi kuwa da ahlinsa ka yi biris, wato ko oho Alhali kowa ya san gida shara-shara ai sai sauro Sai ka shiga ciki ka yi mulumbukui har da minshari Shi kuwa ka bar shi a waje tsawon dare yana rawar dari Sau da yawa yanata kai-kawo, a gidansa ya zam bare Wa ya jawo masa, in ba kai ba! Duka har da su ta'bare Har in za ka fita a dinga "Kar fa ka bar shi ya shigo" Kun ji dabi'a irin ta dan'Adam mugunta kwando-kwando Ko da shi ke banga laifin ka ba Lado "Kowa ya kwana lafiya, shi ya so" Tijjani M. M. (c) 191111

You might also like